Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Na Tallafawa 'Yan Kasuwa A Jihar Kebbi


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Duk da barazanar da ake fuskanta ta cutar coronavirus ko murar mashako karo na biyu a duniya, Gwamnatin Najeriya ba tayi kasa a gwiwa ba na ci gaba da taimakawa jama'a domin farfadowa daga rubushin da suka samu sanadiyar cutar karon farko.

A jihar Kebbi dake arewa Maso yammacin kasar ‘Yan kasuwa ne suke murnar samun bashin naira biliyan biyu domin farfadowa da kasuwancin su.

“Yan kasuwa dari biyar da arba'in da shida ne suka amfana da samun bashin kudi daga naira miliyan daya zuwa biyar karkashin shirin bayar da bashin ta hukumar Nirsal domin farfadowa da sana'o'in su da suka tabarbare sanadiyar cutar murar mashako.

Babban lauyan gwamnati kuma Ministan Shara'a na Najeriya Abubakar Malami ya ce domin saukaka samar da bashin ga jama'ar, wata kungiya dake fafatukar samar da ci gaban al'umma ta Hadimiya ita ce ta shiga gaba wajen nemo wadannan kudade ga mutanen.

Ya ce “gwamnatin tarayya tana sane da matsalolin da ‘yan kasuwa suka fada ciki sanadiyar annobar coronavirus, dalilin haka ne kuma take aiki tare da wannan kungiya ta Hadimiya domin ci gaba da tallafawa al’umma.

Ko bayan wannan, ministan ya ce bisa ga saukaka matsalar rashin samun ruwa ga jama'a kungiyar tayi fafatukar samar da riyojin burtsaste 150 a sassa daban daban na jihar ta Kebbi.

Faruk Abubakar Mai Sudan shine sakataren kungiyar Hadimiya ya ce wannan aikin kamar soman tabi ne daga shirin da take da shi na samar da ci gaban rayuwar al'ummar jihar Kebbi.

Duba da cewa akwai masu na neman irin wannan tallafin bashi da yawa da basu same sa ba, wadanda suka amfana da samun bashin ta hanyar wannan kungiyar sun bayyana farin cikin su..

Da yake an rarraba takardun amincewar bayar da bashin ga mutanen abin jira a gani shine shigowar kudin da kuma yadda zasu yi amfani da su wajen habaka kasuwancin su duk da yake cutar murar mashako karo na biyu na barazana ga jama'a a kasashen duniya.

Ga dai rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Karin bayani akan: Muhammadu Buhari, Najeriya, Jihar Kebbi, da Nigeria.

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG