Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwmantin Tarayya ta jajantawa al’ummar karamar hukuma Kajuru a jihar Kaduna


Ministan Harkokin Cikin Gida Abdiulrahman Bello Dambazau

Wata tawagar gwamnatin tarayya ta kai ziyara a karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna inda wasu yan pashi da makami suka kai hari a ranar sha bakwai ga wannan wata na Yuli.

Ministan harkokin cikin gida Laftan Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya shine ya jagoranci tawagar wannan ziyara gani da ido.
Ziyarar ta tawagar gwamnatin tarayyar ta biyo bayan alwashi da gwamnatin ta sha na gani ta zakulo wadanda suka tabka danyen aikin wanda ya kai ga hallaka mutane da dama kana suka tarwatsa shanu a karamar hukumar Kajuru na Kaduna.
Ministan Cikin gidan Abdulrahman Dambazau ya yiwa jama'a gargadi, da su kiyaye daukar doka a hannu wurin kai hari ramuwar gayya saboda gwamnati tana iya kokarinta wurin kama maharani ta kuma hukuntasu.
Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru Ahmed el-Rufai yana cikin tawagar gwamnatin tarayyar. Gwamnan ya isar da ta’aziyar shugaban kasa Muhammadu Buhari game da wannan rashi kana shugaban kasar ya nuna rashin jin dadinsa ga wannan aika aika. Gwamnan na Kaduna ya ci gaba da yin kira da a zauna lafiya kada wani ya dauki doka a hannu, saboda su jami’an tsaro sun ce sun san yan pashin da suka kai harin.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG