Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Ce Za Ta Inganta Garuruwan Da Aka Kwato Daga Hannun Boko Haram


ADAMAWA: 'Yan gudun hijira da za'a rufe sansaninsu

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace zata samar da ababen more rayuwa ga garuruwan da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram.

A dai-dai lokacin da mutane ke komawa garuruwan su na asali a tarayyar Najeriya biyo bayan nasarar da aka samu da yaki da Boko Haram, gwamnatin tarayya tace zata kyautata yanayi a wadannan yankunan da wannan lamari ya shafa domin mutanen wadannan wuraren su samu natsuwa.

Mutanen dai sun jima cikin damuwa na hasarar da suka yi ta ‘yan uwansu da dukiyoyin su abinda yasa gwamnatin tace wajibi ne ta kyautata rayuwar su musammam ma wajen samar musu ababen more rayuwa.

Wannan ne yasa Mataimakin shugaban kwamitin kula da ‘yan gudun hijiran, Alhaji Tijjani Tumsa ya shaidawa wakilin muryar Amurka Nasir Adamu El-Hikaya cewa sun fara magana da masu ruwa da tsaki a harkan ilmi domin gyara makarantu a wadannan jihohin da lamarin ya shafa.

Yace kwamitin kula da komawar ‘yan gudun hijiran zai taimakawa wadannan mutanen da ganin sun sake gina gidajen su.

Ga Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani 2’54:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG