Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnoni Sun Nemi Cire Dokar ta Baci


Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako, daya daga cikin gwamnonin da jihohinsu ke cikin dokar ta baci.
Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako, daya daga cikin gwamnonin da jihohinsu ke cikin dokar ta baci.

Yayin da saura 'yan kwanaki wa'adin dokar ta baci da aka kakabawa jihohin Adamawa, Borno, da Yobe ke karatowa, gwamnoni johohin uku sun nemi gwamnatin tarayya ta cire dokar maikon sabuntata kamar yadda tayi a baya.

Bayan wani taro da gwamnonin Adamawa da Borno da Yobe suka yi, wadanda jihohinsu ke cikin dokar ta baci,sun cimma matsaya daya akan cewa kada a sake sabunta wa'adin dokar.

Gwamnonin sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka nemi a janye dokar ta bacin kacokan a kuma sauya lale da yakin da ake yi da 'yan ta'ada.

Alhaji Ahmed Sajoh daraktan yada labaran gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya bayyana dalilan da gwamnonin suka bayar na son a janye dokar. Yace idan har dokar ta baci bata cimma burinta ba bayan shekara daya to kamata yayi a sauya salo. Watakila sauya salon ka iya kaiga nasara. Abubuwan da suka faru cikin shekara daya yakama su zama darusan da zasu kaiga samun maganin ta'asar da a keyi ba lallai sai an sake sabunta dokar ba.

Haka kuma gwamnonin sun nemi hukumar zaben kasa wato INEC tayi koyi da kasar Afghanistan wadda ta gudanarda zabe duk da barazanar da kungiyar Taliban tayi. Kungiyar tayi barazanar kai hari idan aka kuskura aka shirya zabe. Amma hukumar zaben kasar da gwamnatin kasar da talakawan kasar sun hada kai sun fito sun yi zaben. Yace mutane sun nunawa 'yantsagera cewa tsagerancinsu ba zai hana mutane kyautata rayuwarsu ba. Haka yakamata INEC da gwamnatin da al'ummomin kasar su yi.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG