Accessibility links

Majalisar Dokokin Gombe Tayi Watsi da Tallafin Nera Biliyan Biyu


Gombe, Najeriya

A cikin jawabin da shugaban kasar Najeriya yayi lokacin da yake bude taron habaka tattalin arzikin jihohin arewa maso gabas yayi alkawarin baiwa yankin tallafin nera biliyan biyu daidai lokacin da aka ce ya warewa jiharsa ta haifuwa nera biliyan talatin lamarin da yasa suka raina kudin

Majalisar dokokin jihar Gombe ta dauki wani mataki a madadin jihohin arewa maso gabas inda tayi watsi da tallafin nera biliyan biyu da shugaba Jonathan yace zai basu domin tallafawa habaka tattalin arzikin yankin.

A wani zama da majalisar ta jihar Gombe tayi ta zantar da kudurin kin amincewa da tallafin nera biliyan biyu da shugaban kasar yayi ma arewa maso gabas alkawari. Dama Jonathan yace kudin zai taimaka wurin shawo matsalar tsaro da habaka tattalin arziki da gyara zamantakewar al'ummomi. Yankin na ganin kudin ba zai tsinanan masu komi ba idan aka yi la'akari da halin da yankin ke ciki

Kakakin majalaisar Inuwa Garba ya bayyana dalilan tsayarda kudurin nasu.Yace idan an lura da irin halin da yankin ke ciki bai kamata a ce gwamnatin tarayya nera biliyan biyu kawai zata ba yankin ba, wato yankin da ya kunshi jihohi shida bayan ana ba wasu jihohi daruruwan biliyoyi. Yace ba'a yi masu adalci ba shi yasa suka yi kudurin kin amincewa da tallafin.

Dangane da ko sun tuntubi sauran jihohin dake cikin yankin, Inuwa Garba yace sun tuntunbesu kuma su ma sun tsayar da shawara daya, wato kin amincewa da kudin tallafin. Bugu da kari sun sanarda duk wakilansu dake majalisun tarayya su isarda sakonsu ga shugaba Jonathan.

Da yake bada amsa kan ko nawa yakamata a basu sai kakakin yace idan ana son a yi masu adalci kowace jiha a ware mata nera biliyan goma cikin kasafin kudin kasa wato biliyan sittin ke nan ma yankin nasu. Wannan shi ne na farko wanda za'a yi anfani dashi akan marasa aikin yi da inganta ilimi da harkokin tsaro.

Mataki na gaba da zasu dauka inji kakakin, 'yan majalisun shida zasu tafi Abuja su gabatarda korafinsu ga majalisar tarayya. Yace suna son su tabbatar masu cewa halin da jihohin arewa maso gabas ke ciki yanzu idan ba'a yi hankali ba zai bazu cikin kasar. Yace yanzu ma rikicin ya fara canza salo a wasu wurare.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.
XS
SM
MD
LG