Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Arewa Na So a Ja Kunnen Nnamdi Kanu


Wasu daga cikin gwamnonin Arewacin Najeriya

Gwamnonin arewacin Najeriya sun nemi takwarorinsu na kudu maso gabashin Najeriya da su ja kunnen matasan yankunansu da ke kalamai masu haifar da rarrabuwar kawuna a Najeriya, musamman ma shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu.

Gwamanonin arewacin Najeriya sun yi kira ga takwarorinsu na kudu maso gabashin kasar, da su tsawatar shugaban kungiyar masu fafitikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu kan irin kalaman da yake yi.

Shugaban kungiyar gwamnonin na arewa, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima shi ne ya yi wannan kira yayin wata hira da yi da Muryar Amurka bayan da ya kammala wani taro da shugabannin kungiyoyin matasan arewa.

“Muna kira ga shugabannin kudu maso gabashin Najeriya, su ma su kira ‘ya’yansu, su Nnamdi Kanu, domin da hannun hagu ake wanke hannun dama, mu za mu sa kannenmu, ‘ya’yanmu su yi abinda ya cancanta a yi. Su ma ya kamata su nasu su bar zagi da muzgunawa mutane.” In ji Shettima.

Wannan kira da shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ya yi na zuwa ne bayan wani zama da suka yi da shugabannin matasan arewa kan wannan batu.

“Mun zauna da shugabannin matasan arewa, mun fahimci juna, kuma insha Allah a cikin satin nan za su dauki matakan da zai faranta ran kowane dan Najeriya.” Ya kara da cewa.

Kungiyoyin matasan arewa sun ce za su ci gaba da tuntubar juna domin warware batutuwan da suka dame su.

Su dai matasan na arewa, sun ba da wa’adin zuwa ranar daya ga watan Oktoba a matsayin ranar da suka bai wa al’umar Igbo da su koma yankunansu a matsayin martani ga kiraye-kirayen da kungiyar IPOB mai fafitikar ganin an kafa kasar Biafra ke yi.

Kuma wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umar kasar.

Saurari rahoton Medina Dauda domin jin cikakken bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG