Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Habasha Ta Kori Jami'an Gidan Yari Guda Biyar


Kasar Habasha ko Ethiopia ta kori jami’an gidan yari guda biyar a wani gidan kurkukun da ake zargin ana aikata rashin imani daga aiki, sakamakon wani rahoto da ya nuna yadda ake cin zarafin mutane da take musu hakkokin su.

Daya daga cikin Jami’ain biyar da aka kora daga aiki yau Alhamis, shine ma shugaban gidan yarin.

Korar ta zo dab kafin kungiyar kare yancin bil’adama ta duniya ta Human Rights Watch ta fitar da rahoton dake nuna yadda ake cin zarafin fursunoni a gidan yarin Ogadan dake yankin Soamli dake gabashin kasar ta Ethiopia.

Rahoton ya hada da shedar fursunonin dake gidan yarin wadanda suka bayyana cin zarafi da muzgunawar da ake yi musu ta hanyar azabtar da su cikin wani kunci da kuma hana su samun kulawar lafiyarsu da abinci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG