Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Habasha Ta Samu Shugabar Kasa Mace


Karon farko kenan da mace ta zama shugabar kasar a kasar Habasha. Sahle-Work Zewde ta fara aiki yau a matsayin shugabar kasa bayan ta kwashe shekaru tana aikin jakadancin kasar.

‘Yan majalisar dokokin kasar Habasha sun zabi wata tsohuwar jami’ar diflomasiyyar kasar Sahle-Work Zewde a matsayin mace shugabar kasa ta farko a kasar dake gabashin nahiyar Afrika.

Ita ce zata maye gurbin Mulatu Teshome, wanda yayi murabus daga mukamin jiya Laraba. Amma sabuwar shugabar ba za ta wuce wa‘adodi biyu na shekaru shida-shida ba akan kujerar mulki.

Sahle-Work, ‘yar shekaru 68 da haihuwa, ita ce jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a Kungiyar Tarayyar Kasashen Afrika. A baya ta taba zama jakadiyar Habasha a kasashen Faransa, da Senegal, da Djibouti, ta kuma shugabanci ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Nairobi.

Fitsum Arega, shugaban ma’aikatan fadar Firayin minista Abiy Ahmed, ya yaba da zaben Sahle-Work yau Alhamis a shafinsa na twitter. Arega ya rubuta cewa “a kasar da maza ke jagorantar yawancin harkoki kamar irin tamu, nadin mace a matsayin shugaba ba kawai yana zaman wani abin koyi bane nan gaba amma ya nuna cewa an dauki mata a matsayin masu fada a ji a harkokin al’umma.”

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG