Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Tattalin Arziki Ta Haifar Da Karancin Magunguna A Zimbabwe


Mata masu ciki a wani asibitin Harare, Zimbabwe,

Matsalolin tattalin arzikin da kasar Zimbabwe ke huskanta, ya haddasa karancin muhimman kayan harhada magunguna a kasar. Jami’ai sun ce karancin magunguna yasa mutane suna zuwa wurin wadanda basu da izinin sayar da magani domin su samu magunguna, kuma hukumomi na bayyana damuwarsu cewa irin wadannan magunguna suna da hadarin gaske.

Bincike ya nuna cewa, Karancin kaya a Zimbabwe ya zarce batun man fetir da wasu kayan abubuwan more rayuwa.

Kungiyar kamfanonin sarrafa magunguna ta Zimbabwe tace bata samun isasshen kudaden kasar waje da zata iya sayo magungunan sankara da cutar sukari da ta hawan jinni da wasu magungunan kashe radadin ciwo.

Idan kuwa ba a iya samun magungunan a wuraren da ya kamata ba, kasuwannin sayar da magugunguna na bayan fage zasu habaka, wadanda tana yiwuwa suna taimakawa amma kuma akwai yiwuwar jefa rayuwar marasa lafiya cikin hadari.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG