Accessibility links

Habila Adamu Ya Tsallake Rijiya Da Baya


Ciwon da Habila Adamu ya samu bayan da 'yan Boko Haram suka harbeshi a ka.

Jihar Yobe na cikin jihohi uku dake karkashin dokar ta baci sabili da aika-aikar kungiyar Boko Haram. Habila Adamu na cikin wadanda kungiyar ta kai ma hari amma Allah ya tsirar da shi.

Habila Adamu wani dan jihar Yobe ya ziyarci Muryar Amurka inda ya bayyana yadda Allah a cikin ikonsa ya sa ya rayu duk da mugun harbin da aka yi masa.

A firar da na yi da shi ya bayyana yadda 'yanbindigan suka shigo gidansa suka harbeshi.Habila ya ce makasudin zuwansa Amurka a wannan lokacin shi ne samun ganawa da yan majalisar dokokin kasar Amurka su yi taimako a kawo karshen tashin hankali a Najeriya.

Ranar 28 ga watan 11 shekarar dubu biyu da goma sha biyu 'yan bindigan suka shiga gidansa suka kirawo shi da matarsa suka yi masa wasu 'yan tambayoyi kana suka harbeshi a ka da AK-47 wajen karfe goma sha dayan dare. Nan aka barshi har ma matarsa ta dauka ya mutu. Sai wanshekare aka kaishi asibiti.

Bayan an harbeshi labarin ya bazu har wata kungiya Voice of Mrtyrs ta samu labari. Ita ce ta shirya ta kawo shi Amurka inda aka yi masa jinya. Yanzu karfe aka sa a kumatunsa domin bindiga ta yi rugu-rugu da kashin gefen fuskarshi na dama.

Habila Adamu ya ce yanzu yana kai da kawo tsakanin Najeriya da Amurka domin ya nemi taimako na yin kokarin shirya zaman lafiya ta wayar da kawunan matasa, shugaban addinai da masu fada aji domin duk abun da ya shafi Najeriya ya shafi duniya.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG