Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadaddiyar Daular Larabawa, Isra'ila Sun Bude Hanyoyin Wayar Tarho


Israel UAE Flags
Israel UAE Flags

Hadaddiyar Daular Larabawa da Isra’ila sun bude hanyoyin sadarwarsu ta wayar tarho a yau Lahadi, a wani mataki da Ministan sadarwar kasar ta Isra’ila ya kwatanta a matsayin muhimmin ci gaba a kokarin da kasashen biyu ke yi na kyautata dangantakarsu.

Babu dai takamaiman lokacin da za a iya cewa an dage haramcin sadarwar ta wayar tarho tsakanin Hadadiyyar Daular ta Larabawa da Isra’ila, amma dai tarihi ya nuna cewa an dade ba a iya yin kira ra wayar tarho a tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ya gwada yin kira daga hadaddiyar daular larabawa zuwa Isra’ila.

Kokarin jin ta bakin hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta hadaddiyar daular larabawa ya cutura.

Rahotanni sun yi nuni da cewa a yau Lahadi ana iya shiga kafafen yada labaran Isra’ila na yanar gizo daga Hadaddiyar daular larabawan, wadanda a da ba iya shiga.

A ranar Alhamis kasashen biyu suka bayyana cimma wata matsaya ta maido da cikakkiyar huldar diplomasiyyarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG