Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bakin Haure Dake Tsallakawa Zuwa Turai Sun Karu A Cikin Shekara


Bakin Haure a kan tekun Italiya
Bakin Haure a kan tekun Italiya

Adadin bakin haure da suka isa gabar tekun Italiya sun ninka adadi na bara, yayin da matsalolin tattalin arziki a Tunisia ke kara iza bakin haure a cikin kwale kwale zuwa tekun Maditareniya, inji ministan harkokin cikin gida Luciana Lamorgese a jiya Asabar.

Sama da mutum dubu 21 suka isa Italiya tsakanin Agustan 2019 zuwa karshen watan Yuli na wannan shekara, adadin day a haura kashi 148 cikin dari, inji ministan, yayin da take jawabi a taron manema labarai na shekara shekara a ranar 15 ga watan Agusta.

Lamorgese ta ce galibin wadanda suka isa gabar tekun sun yi zuwan kan su ne, abin da hukumomi suka ce yana da wahala a dauke su da kananan jiragen ruwa, ba kamar wadanda aka ceto su daga kan teku zuwa gabar tekun ba. Yawancin su sun isa ne a tsibirin maditareniya na Lampedusa dake kudancin Italiya.

A cikin watanni 12, sama da mutane dubu biyar kawai ne aka ceto su, yawanci da jiragen ruwa na kungiyoyi masu zaman kan su, a cewar wasu alkalumma daga ma’aikatar harkokin cikin gidan.

Sama da kashi 80 cikin dari na bakin haure da suka isa Italiya, sun tashi ne daga kasashen Tunisia da Libya, kamar yanda wasu bayanai suka nuna, kana matsalar Tunisia kuma ta kara yawan mutane masu neman tsallaka tekun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG