Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadakar Jam'iyyun Siyasar Habasha Sun Zabi Abiy Ahmed Shugabansu


Abiy Ahmed shugaban hadakar jam'iyyun Habasha wanda zai zama Firayim Ministan kasar
Abiy Ahmed shugaban hadakar jam'iyyun Habasha wanda zai zama Firayim Ministan kasar

Zaben da hadakar jam'iyyun Habasha suka yi wa Abiy Ahmed ya share masa hanyar zama Firayim Ministan kasar ya maye gurbin wanda ya yi murabus

Hadakar jam'iyun siyasa dake mulki a Habasha ko Ethiopia, sun zabi Abiy Ahmed a zaman shugaban su,kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka yi bayani.

Matakin ya share fage ga Ahmed ya zama Firayim MInistan kasar na uku cikin shekaru 23.

Ahmed zai maye gurbin Hailemarima Desalegn, wanda ya ajiye aiki cikin watan Jiya a yayinda kasar take ci gaba da fuskanta rigingimun siyasa a duk fadin kasar.

Ahmed dan shekaru 41 da haifuwa, bai cika shekaru 10 a fagen siyasa ba. Kamin ya zama wakili a majalisar wakilan kasar a shaekarar 2010, ya rike mukami leftanar kanal a rundunar sojin kasar.

Ahalinda ake ciki kuma mutane da ake zargin mayakan sakai ne sun harbe suka kashe wata 'yar majalisa Rukiya Abshir Noor, a gidanta dake Mogadishu jiya Talata.

Wani jami'in 'Yansandan kasar ya gayawa Sashen Somalia na Muryar Amurka cewa, 'yar majalisar ta sami munanan raunuka, aka garzaya da ita zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG