Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin Mota Ya Kashe Mutune Uku A Jihar Osun


Wani hadarin mota da aka yi a jihar Osun yayi sanadiyar asarar rayukan mutane uku da kuma raunata mutum guda.

Kwamandan hukumar kiyaye faruwar hadura ta jihar Osun, Alhaji Umaru Ibrahim, shine ya tabbatar da faruwan hadarin, inda yace ya faru ne kan hanyar dake tsakanin mahadar Iwara zuwa garin Ibeto. Ya kara da cewa kasancewar yanayin kyawun hanyar yasa ake yawan samun hadura masu yawa.

Cikin mutanen da suka mutu a wannan hadari sun hada da maza biyu da mace ‘daya. Gudu da motocin biyu ke yi da ya wuce kima shine yayi sanadin taho mu gama.

Daga karshe Alhaji Umaru Ibrahim, yayi kira ga jama’a da rinka kula yayin tafiya kan wannan hanya, kuma idan direbobi na guda alhaki ya rataya kan fasinjoji da su yi musu magana don su rage gudu domin kiyaye faruwar hadari da salwantar rayuka.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG