Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Najeriya INEC Zata Yi Nazari Akan Inganta Ayyukanta


Nick Dazan daraktan labarai da sanarwa na hukumar zabe INEC
Nick Dazan daraktan labarai da sanarwa na hukumar zabe INEC

Yayinda yake zantawa da Muryar Amurka daraktan labarai da hulda da jama'a na hukumar INEC, Nick Dazan ya fada cewa hukumar zata yi taro a kebe inda su ma'aikatan zasu yi nazari akan abubuwa da dama domin tabbatar da ingantacen zabe nan gaba

Inji Dazan akwai ayyuka da dama da hukumar zabe ke son ta aiwatar tsakanin wannan shekara zuwa ta dubu biyu da ishirin da daya.

Na farko zasu koma aikin yiwa mutane rajista saboda wadanda basu samu sun yi ba can baya a basu damar yi yanzu. Biye da wannan shi ne cigaba da raba katuna na dindindin da hukumar bata gama rabawa ba. Kafin a soma yin rajista hukumar zata fitar da jadawalin aikin.

Wani abu kuma da hukumar zata yi shi ne yiwuwar kirkiro cibiyoyin zabe a wasu wurare. Tun shekaru 19 da suka gabata lokacin da aka kirkiro cibiyoyin zabe 120,000 ba'a sake kirkiro wasu kuma ba. Yace akwai inda ake samun cunkoso lokacin zabe kuma akwai biranen da aka samu yawan mutane. Unguwanni daban sun taso. Mr. Dazan yayi misali da Abuja inda babu cibiyoyin zabe sai lokacin zabe mutane su rasa wurin zuwa su kada kuri'a.

INEC zata yi nazari akan kirkiro sabbin mazabu yadda yawan al'umma a mazabun kasar zai zo kusan daya. Yanzu matsayin mazabun ba daya ba ne. Misali a Legas mazabar Alimosho tana da yawan mutane fiye da kowace mazaba a Najeriya amma wakili daya suke dashi a majalisa.Wannan ba adalci ba ne garesu.

Dangane da cewa watakila bayan sun kammala aikinsu wasu jihohi zasu samu karin wakilai sai Nick Dazan yace hakan na yiwuwa amma shi ba zai yiwa kowa alkawarin haka ba sai sun gama aiki an bayyanawa kowa tsarin da suka fito dashi.

Baicin wadannan abubuwa akwai tunanen ba 'yan kasar dake kasashen ketare damar kada kuri'unsu lokacin zabe a wuraren da suke. Kawo yanzu Najeriya nada mutane fiye da miliyan 15 a kasashen waje. Amma yin hakan sai gwamnati ta amince.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

XS
SM
MD
LG