Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin Tanka Ya Kashe Fiye Da Mutane Ashirin A Badun

Akalla fiye da mutane ashirin ne wuta ta kona kurmus,sakamakon hadarin motar dakon kaya da auku a Jumma’a a unguwar Adeleju dake kan titin Express a cikin birnin Ibadan.

Akalla fiye da mutane ashirin ne wuta ta kona kurmus,sakamakon hadarin motar dakon kaya da auku a Jumma’a a unguwar Adeleju dake kan titin Express a cikin birnin Ibadan.

Shaidun gani d a ido suka ce kwatsam suka ga wuta tashi tana ci babu kakkautawa, da suka bar aiki domin su kai doki sai suka ga babbar motar daukar Mai ce ta fadi take cin wuta.

Daya daga cikin shaidun yace,mutane takwas dake cikin tankar, da wasu mutane goma sha takwas cikin wata Bus duk sun kone kurmus.

‘Yan kwana-kwana sun basu ji dadin zuwa ba,domin jama’a sun bayyana bakin cikinsu,saboda sunzo bayan wutar ta gama yin barna.

Akalla motoci talatin ne wutar kona.

Hadarin Tanka Ya Kashe Fiye Da Mutane Ashirin A Badun

XS
SM
MD
LG