Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadin Gwiwar Yan Sandan Najeriya Tare Ali Kwara Na Ci Gaba Da Samun Nasara


A wani sabon yunkuri na yaki da yan fashi da makami da barayin shanu, da kuma masu satar mutane suna garkuwa da su domin neman kudin fansa, yanzu haka rundunar yan Sandan Najeriya ta kaddamar da wata hadaka da shahararren mai kama barayin nan Ali Kwara.

Bisa ga dukkan alamu dai kwalliya na ci gaba da biyan kudin sabulu a aikin sintirin hadin gwiwar da rundunar yan Sandan Najeriya ke yi tare da yan sa kai na Ali Kwara a jihar Adamawa. Domin kawo yanzu ma ana ci gaba da bankado yan taba gari na yan fashi da makami da barayin Shanu har ma da wadanda ke garkuwa da mutane domin kudin fansa.

Ali Kwara, yace kawo yanzu suna samin nasara a aikin da suke yi a jihar Adamawan, inda ma ya fadi nasarorin da suka samu cikin kwanakin nan wanda ya hada da sumamen da suka kai wani kauye a karamar hukumar Maiha, har sukayi nasarar samo bindigogi guda hudu, aka kuma samo bayanan kan wasu barayin dake karamar hukumar Fufure, wanda suma aka kai musu hari.

Kakakin rundunar yan Sanda na jihar Adamawa DSP Usman Abubakar, yayi tabbatar da faruwar wannan artabu da yan Sanda na musammam masu yaki da fashi da kamani tare da yan sa kai karkashin jagorancin Ali Kwara.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

XS
SM
MD
LG