Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamisu Breaker, Namenj Sun Cashe A Liyafar Yusuf Buhari Da Amaryarsa Zahra

Namenj da Hamisu Breaker a lokacin da suke cashewa a bikin Yusuf Buhari da Zahra (Instagram/Breaker)
Namenj da Hamisu Breaker a lokacin da suke cashewa a bikin Yusuf Buhari da Zahra (Instagram/Breaker)

Breaker ya rera wakar ‘Jaruma’ kana sun cashe a wakar ‘Da Ma’ da Namenj ya yi wacce ya gayyato Breaker suka yi tare.

Fitattun mawakan Kannywood Hamisu Breaker da Namenj sun baje kolin wakokinsu a bikin dan shugaban kasa Yusuf Buhari da amaryarsa Zahra Nasir Ado Bayero.

A ranar Juma’ar da ta gabata aka daura auren a garin Bichi da ke jihar Kano a arewacin Najeiriya.

Mata da suka halarci liyafar Yusuf da Zahra a lokacin da Namenj da Breaker suke cashewa (Instagram/Namenj)
Mata da suka halarci liyafar Yusuf da Zahra a lokacin da Namenj da Breaker suke cashewa (Instagram/Namenj)

Breaker ya rera wakar ‘Jaruma’ kana sun cashe a wakar ‘Da Ma’ da Namenj ya yi wacce ya gayyato Breaker suka yi tare.

Tun bayan da aka daura auren a ranar Juma’a aka bude shagulgulan biki tun daga Kano, inda aka dangana da Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya inda a nan mawakan suka cashe.

Yusuf Muhammadu Buhari da Amaryasa Zahra Nasiru Ado bayero
Yusuf Muhammadu Buhari da Amaryasa Zahra Nasiru Ado bayero

A lokacin liyafar, an ga masoyan wakokin mawakan biyu suna ta cashewa tare da bin wakar ‘Da Ma’ yayin da ake nishadantar da su.

Hamisu Breaker da Namenj na daga cikin mawakan da tauraronsu ke haskawa a fagen wakokin Hausa na zamani a Najeriya da sauran kasashen Hausa.

Yadda Aka Yi Shagalin Bikin Yusuf Buhari Da Amaryarsa Zahra Nasir Ado Bayero

Yadda Aka Yi Shagalin Bikin Yusuf Buhari Da Amaryarsa Zahra Nasir Ado Bayero
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG