Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Juyayi Wadanda Aka Kashe Jiya Lahadi a Jihar Florida


Omar Mateen wanda ya kashe mutane 50 ya jikata wasu 53 a wurin shakatawar 'yan luwadi a birnin Orlando dake jihar Florida nan Amurka

Dubban mutane ne 'yan luwadi da wadanda ba 'yan luwadi ba, suka yi jerin gwano rike da wutar kendir a manyan biranen Amurka masu yawa jiya Lahadi domin tunawa da mutane 50 da aka harbe aka kashe su a wani club, a zaman hari mafi muni na kisan kan mai uwa dawabi a tarihin Amurka.

Dan shekaru 29 da haifuwa mai suna Saddiqui Matten, haifaffen Amurka da iyayensa suka zo daga Afghanistan ne ya bude wuta da asubahin jiya Lahadi a club din dake birnin Orlando. Mutane 53 sun jikkata wasu suna cikin mawuyacin hali. Club din galibi na 'yan luwadi ne.

Shugaban Amurka Barack Obama, a fusace, wanda kuma yake juyayi da nuna alhini, yayi magana da rana jiya, inda ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda aka kashe cikin dare a club din.Wannan shine karo 15 da Mr. Obama yake jawabi ga Amurka bayan da aka kai hari irin na kan mai uwa da wabi tunda ya kama mulki.

Obama yace kisan, "shine hari irin wannan mafi muni a tarihin Amurka." Yace Darektan hukumar bincken manyan laifuffuka ta Amurka watau FBI James Comey, yayi masa bayani, yace kodashike yanzu aka fara bincike, akwai isassun bayanai da zasu sa a ayyana cewa wannan ta'addanci ne da kuma nuna kiyayya.

Shugaban na Amurka yace babu ta'addanci ko kiyayya da zata canza mu," sai dai ya kara da cewa duk harin da aka kaiwa ba Amurke daya, tamkarar hari ne kan dukkan Amurkawa.

Ahalinda ake ciki kuma, musalmai a duk fadin Amurka suna bayyana alhini da goyon bayansu ga 'yan uwan wadanda wannan mummunar hari ya rutsa da su a birnin Orlando na jihar Florida.

Shugaban wata cibiyar Islama dake kusa da nan birnin Washington DC, ya gayawa Sashen Afghanistan na Muryar Amurka cewa, "kashe mutane da basu aikata komi ba, hali ne na raggwanci, da duk musulmi ko Bil'Adam zai yi Allah wadai da shi.

XS
SM
MD
LG