Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Kokarin Kashe Gobarar Daji a Tsaunin Kilimanjaro


Ma’aikatan kashe goba sun shiga rana ta biyar yau Alhamis a kokarinsu na kashe gobarar daji a wani gandu a tsaunin Kilimanjaro, wanda shine mafi tsayi a Afirka.

Ministan Albarkatun Kasa da Yawon Bude Ido na Tanzania, Hamisi Kigwangalla, ya fada jiya Laraba cewa wutar tana barazana ga yankin muhallin halittu, wanda ke dauke da halittu daban daban da suka hada da tsuntsaye, macizai da kuma dangin kadangaru.

Kigwangalla ya ce busasshen yanayi, iska mai karfi, da kuma wurin da gobarar ta tashi na kawo cikas wajan kokarin shawo kanta.

Jaridar Citizen ta rawaito cewa Kigwangalla ya fada jiya Laraba cewa gwamnati za ta sayo jirage masu saukar ungulu domin karfafa yaki da gobarar daji.

Ya kuma umarci Hukumar Kula da Gandun Daji ta Tanzania da ta ingata kayakinta na kashe gobara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG