Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takarar Ngozi Okonjo-Iweala: Buhari Zai Shiga Kamfe


Dr. Ngozi Okonjo-Iweala

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana niyar shiga gaba wajen yi tsohuwar Ministar Kudi da tattalin arziki Dr Ngozi Okonjo-Iweala kanfen yakin neman zabe a takarar jagorantar Kungiyar Cinikayya ta duniya

Shugaba Buhari ya bayyana niyarsa ta yin tsayin daka da kuma kamun kafa domin ganin ‘yar takarar ta Najeriya ta cimma nasarar lashe wannan zaben da ke cike da tarihi. Ya ce Najeriya zata dauki dukan matakan da suka dace da kuma amfani da duk dama da ta ke da ita, wajen ganin Ngozi Okonjo-Iweala ta kai ga nasara.

Shugaban Najeriyan ya wallafa a shafinsa na twitter bayan karbar bakuncin ‘yar takarar a fadar shugaban kasa ta Aso Rock cewa, “Za mu yi dukan abinda muka iya, mu tabbata Ngozi Okonjo-Iweala ta zama Darekta-Janar ta Kungiyar Cinikayya ta Duniya WTO. Ta cancanci wannan. Zan ci gaba da neman goyon bayan shugabannin kasashen duniya a madadinta. Duk wayar da ake bukatar bugawa, duk wasikun da ake bukatar aikawa, Zan yi.”

‘Yar takarar ta yaba irin goyon bayan da shugaban kasar da kuma gwamnatinsa ke bata. Tace shugaba Buhari da ministocinsa musamman na ma’aikatun harkokin waje da kuma na Masana’antu, Ciniki da zuba jari, suna aiki ba dare ba rana domin ganin ta yi nasara. Ta kuma yi kira ga shugaba Buhari ya kara tsaya mata ta wajen sake tura wasiku da kiran shugabannin ta wayar tarho, da kuma godewa wadanda suka nunawa Najeriya goyon baya, domin ta samu iya kada abokiyar takararta ‘yar kasar Koriya.

A jiya Litinin tsohuwar Ministar kudin ta gana da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa ta Aso Rock sai dai duk da yake ba a bayyana dalilin ganawar ba, masu kula da lamura suna kyautata zaton bashi rasa nasaba da takarar ta.

A cikin wata kasida da ta gabatar a wani taro da aka gudanar a birnin Geneva, Ngozi Okonjo-Iweala, wadda take daya daga cikin ‘yan takarar da ke kan gaba a wannan takarar, wadda kuma a halin yanzu take shugabantar kwamitin samar da rigakafi na hadin guiwa GAVI, ta bayyana niyarta ta bada gudummuwa a yaki da annobar Coronavirus. Bisa ga cewarta, akwai dangantaka tsakanin kula da lafiyar al’umma da harkokin cinikayya sabili da haka yaki da cutar ci gaba ne ga kowa.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala tana yakin neman zabe
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala tana yakin neman zabe

A gangamin yakin neman zabenta, ta wallafa a shafinta na twitter cewa “Harkokin cinikayya na da ikon ceton rayuka da kuma amfanar kowa. Ta hanyar yin garambawul ga Kungiyar Cinikayyar ta Duniya ne kawai za mu iya tabbatar da cewa, ta taka rawar gani a yaki da annobar CODVID19 da kuma farfado da tattalin arziki.”

Ngozi Okonjo-Iweala, ta fara kara samun kwarin guiwa a takarar lokacinda aka tashi tsaye ana ta yi mata tafi bayan ta gabatar da kasida a wurin taron inda abokiyar takarar ta mace ‘yar kasar Kenya ita ma ta gabatar da kasida.

Dangane da rawar da zata taka wajen kawo karshen takun saka da ake yi a fannin cinikayya tsakanin Amurka da kasar China, an ambaci ta bakin tsohuwar Ministar kudin Najeriya na cewa, matakan da zata dauka na kawo karshen matsalar ba mawuyacin abu ba ne idan aka kwatanta da fadi tashin da ta yi na ceto mahaifiyarta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da ita da nufin neman kudin fansa. Ta kuma jadada cewa, bata fargaban shiga gaba wajen dinke barakar dake tsakanin manyan kasashen masu karfin tattalin arziki da masana’antu.

Yoo Myung-hee da Ngozi Okonjo-Iweala
Yoo Myung-hee da Ngozi Okonjo-Iweala

Ranar Litinin Kungiyar Tarayyar Turai mai membobi 27 ta bayyana goyon bayan fafatawa tsakanin Ngozi Okonjo-Iweala, da Yoo Myung-hee a zagayen karshe, kafin ranar alhamis Ngozi Okonjo-Iweala da abokiyar takatarta ‘yar kasar Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee suka shiga zagayen karshe na zaben, yayinda ‘yar takarar kasar Kenya Amina Mohamed ta gaza samun goyon bayan ci gaba da takara.

afirka-kungiyar-kasuwanci-ta-duniya-za-ta-samu-shugaba-mace-ta-farko-da-wasu-sauran-labarai

wace-ce-za-ta-zama-shugabar-wto-tsakanin-ngozi-okonjo-iweala-da-yoo-myung-hee

Zaben wadannan matan biyu zuwa zagayen karshe na takarar manuniya ce cewa, kungiyar ta yi niyar zaben mace ta shugabanci kungiyar da maza suka mamaye.

Tuni kungiyoyi da daidaikun jama’a suka fara tura sakonnin taya murna da fatar alheri ga ‘yar takara Ngozi Okonjo-Iweala da tuni ta shiga tarihi, da wucewa zuwa matakin karshe a takarar.

Muna taya Mrs. Ngozi Okonjo-Iweala ta Nigeria , murna, wadda ta shiga zagaye na gaba na zama sabuwar Darekta-Janar ta WTO . Idan ta lashe zabe, zata zama mace ta farko daga kungiyar OACPS da za ta rike wannan mukamin.

Shima shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika ya aika da nasa sakon taya murnar ta hanyar sadarwar twitter.

Mai girma Shugaba Matamela Cyril Ramaphosa yana taya Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta Tarayyar Najeriya murnar hayewarta zuwa zagaye na gaba kuma na karshe a zaben Dareka-Janar na Kungiyar Cinikayya ta Duniya(WTO).

Kungiyar da aka kafa ranar 2 ga watan Janairu, shekara ta 1995, tana da membobin kasashe 164 kuma tana sa ido a kan kashi casa’in da takwas na harkokin kasuwancin duniya. I zuwa yanzu, ba a taba samun mace ko kuma wani daga nahiyar Afrika da ya shugabanci Kungiyar Cinikayyar ta duniya ba tunda aka kafa ta. Idan aka zabi Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar Kungiyar, zata yi tarihi ta fuskoki da dama, da suka hada da kasancewa ‘yar Afrika ta farko, kuma mace ta farko da zata shugabanci Kungiyar.

Shugaban kungiyar na karshe Roberto Azevêdo ya sauka daga mukamin Darekta-Janari din kungiyar ranar 31 ga watan Agusta, 2020, shekara guda kafin cikar wa’adin shugabancinsa. Bayan ya sanar a watan Mayu cewa zai ajiye aiki, aka fara daukar matakin zaben wanda zai gaje shi. Gwamnatocin kasashe takwas suka tsaida ‘yan takara da suka hada da’yar takarar da Najeriya ta tsayar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala tsohuwar darekta a babban bankin Duniya kuma wadda ta yi Ministar kudi har sau biyu, mace ta biyu da aka tsayar takara daga nahiyar Afrika.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG