Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Babu Wanda Ya Dauki Alhakin Hare Haren Saudiya


Harin da aka kai Saudiya
Harin da aka kai Saudiya

Hare haren kunar bakin waken da aka kai a Saudiyya ya shafi manyan biranen kasar a jiya Litinin, ciki har da wanda aka kai a kusa da masallacin Manzon Allah tsira da amince su tabbata a gareshi, wanda ya halaka mutane hudu ya kuma raunata wasu mutane biyar.

Harin na Madina ya faru ne a wani shingen biciken abababan hawa da ke wajen daya daga cikin muhimman wurare na Musulmi.

Miliyoyin Musulmi ne su ke halartar wannan wuri a duk shekara a lokacin aikin hajji.

Ministan aikace-aikacen cikin gida, ya ce maharin ya ta da bam din ne bayan da wasu jami’an tsaro suka tunkare shi.

A jiya Litinin, masallacin ya kasanae cike makil da jama’a, yayin da ake shirye shiryen bikin sallah karama.

Duk da harin da aka kai, kafofoin yada labaran Saudiyya sun nuna hotunan jama’a suna ci gaba da tururuwa zuwa masallacin.

Har ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari.

Hukumomin na Saudiya har ila yau na ci gaba da binciken wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallacin ‘yan Shi’a a gabashin birnin Qatif, inda ministan cikin gidan ya ce an gano wasu sassan jikin mutane uku, amma ba a gane ko su wanenene ba.

XS
SM
MD
LG