Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla Uku Sun Mutu, Ciki Har Da Dan Kunar Bakin Wake Kusa Da Masallacin Annabi


Wani bam na kunar bakin wake ya tashi a wani wurin da ake binciken mutane kafin su shiga cikin Masallacin Annabi (saw) a Medina, a kasar Sa'udiyya.

Bidiyon farko na harin da aka gani a gidan telebijin na al-Arabiyya, ya nuna wuta tana ci a wajen harabar Masallacin, inda aka ga gawar mutum guda.

Daga bisani, gidan telebijin na al-Arabiyya yace mutane akalla uku sun mutu, cikinsu har da mutumin da ake ji shine dan kunar bakin waken da kuma wasu jami'an tsaro guda biyu.

Masallacin na Medina, wanda shine na biyu cikin wuraren da suka fi Tsarki ga Musulmi, nan ne kabarin Annabi Muhammad (saw) yake.

Miliyoyin Musulmi su na ziyartar wannan Masallaci a kowace shekara.

XS
SM
MD
LG