Accessibility links

Har Yanzu Cutar Zazzabin Cizon Sauro Yana Cigaba Da Kashe Yara A Nijar


Ana bama dan yaro maganin cutar cizon sauro

Har yanzu ana samun yaran da kan rasa rayukansu a baban asibitin Maradi a jamuhuriyan Nijar, a sakamakon cutar zazzabin cizon sauro.

Har yanzu ana samun yaran da kan rasa rayukansu a baban asibitin Maradi a jamuhuriyan Nijar, a sakamakon cutar zazzabin cizon sauro.

Dr. Ati Hassan na baban asibitin Maradi ya fadi cewa, "matsalar da ta fi sha wa yara kai ita ce zazzabin cizon sauro. Kuma kowane yini kamar yara 70 ne ke zuwa asibiti."

Dr. Hassan ya kara cewa ana samun yara wadanda suke rasa ransu saboda da cutar zazzabin. Wadansu yaran ma kafin su iso asibiti sun riga sun rasa ransu. Yace, wani lokaci ana samun yara har 5 da suka rasa ran su saboda da cutar zazzabin cizon sauro a asibitin.

Ya kuma kara cewa, da shike mutane da yawa ke kawo yara marasa lafiya, yawancin lokaci ma'aikatan asibitin suna fama da taimakawa dukan jama'a. Ya ce ma'aikatan asibitin sunyi kadan, kayan aiki sunyi kadan, kuma magani yayi kadan. Ya bayyana wa jama'a cewa ba sai baban likita bane kawai za a rika zuwa domin neman taimako domin marasa lafiya. Ana iya zuwan wurin likita a karamin asibiti domin a rubuta maganin da ya dace.
XS
SM
MD
LG