Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harbi Kan Mai Uwa Da Wabi a Potiskum


Wani Dan Bindiga Ya Tada Bam

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa wani dan bindiga ya kai hari a wata makarantar horar da harkokin mulki da kasuwanci a Potiskum.

Wani dan bindigar da ake kyautata zaton dan kungiyar Boko Haram ne ya kai hari a wata makarantar da ake koyar da harkokin mulki da kasuwanci wato college of administration and Business Studies a turance dake garin Potiskum a jahar yobe.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar dan bindigar ya bude wuta ne kan mai uwa da wabi tun daga bakin kofar shiga makarantar har ya kaiga kutsawa cikin harabar makarantar.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, dalibai da wasu ma’aikatan makarantar sunyi kokarin far ma dan bindigar a yayin da yake harbi kan mai uwa da wabi da kuma yinkurin tada wani bam dake daure a jikin sa, sai dai basu sami cin nasarar yin hakan ba.

kamar yadda sauran bayanai suka nuna, dan bindigar ya hallaka kansa da kuma raunata mutane guda takwas. kuma bam din ya tashi a jikin sa ne a yayin da yake kokarin kusawa inda taron jama'a suke a cikin makarantar.

A yanzu haka, daliban da harsashin yayi wa rauni su takwas na karbar magani.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

Harbi Kan Mai Uwa Da Wabi a Potiskum - 7'17"
please wait

No media source currently available

0:00 0:07:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG