Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Haren Bindiga Mafiya Muni Da Aka Taba Kaiwa A Tarihin Amurka


Jami’an ‘yan sanda a birnin Las Vegas ta Jihar Nevada anan Amurka sun ce harin da wani mutum ya kai a wani gidan rawar kidan Kaboyi a daren jiya Lahadi har ya hallaka sama da mutane 58, ya kuma jikkata sama da mutum 500, shine harin harbin bindiga mafi muni a tarihin Amurka.

Ga jerin kididddigar hare-haren da aka kakkai anan Amurka:

  • Yuni 2016: Dan bindiga ya kashe mutane 49 a wani gidan rawar maza da mata manema jinsi guda a birnin Orlando an Jihar Florida.
  • Disamba 2015: Wasu ma’aurata sun bindige mutane 14 bayan farwa wani ofishin ayyukan taimakon al’umma, inda maharani suka sheka lahira sakamakon barin kwuta da ‘yan sanda.
  • Nuwamba 2015: An sami damke wani dan bindigar da suka yi doguwar fafatawar harbe-harbe da ‘yan sanda, bayan ya kashe mutane uku a wani asibitin kula da lafiyar mata a Colorado.
  • Oktoba 2015: An kashe wani dan bindiga a musayar wuta da ‘yan sanda bayan ya bindige mutane tara a Kwalejin Al’umma ta Oregon.
  • Yuli 2015: Wani dan bindigar ya kashe mutane biyar a wata civiyar ajiyar sojin ruwan shirin ko ta kwana a Jihar Tennessee, inda daga baya ‘yan sanda suka bindige shi.
  • Yuni 2015: Haka kuma wani dan bindigar yana zaman jiran shari’a bayan da ya kashe mutane tara a wata Coci da ke Carolina ta Kudu ya kuma tsere amma aka damko shi washe gari.
  • Mayu 2015: An kashe mutane tara a wata musayar wutar da aka samu tsakanin wasu kishiyoyin kungiyar matuka Babura da kuma ‘yan sanda a wani gidan cin abinci da ke Jihar Texas.
  • Oktoba 2014: Wani matashi ya bindige matasa hudu, ciki har da ‘yan uwansa guda biyu, daga baya kuma ya kashe kansa a wata babbar makarantar sakandaren jihar Washington.
  • Satumba 2013: Wani dan bindiga dadin ya kashe mutane goma sha biyu a wani sansanin sojin ruwa dake Washington kafin a samu bindige shi a musayar wuta da ‘yan sanda.
  • Disamba 2012: A Jihar Connecticut wani dan bindiga ya hallaka mutane 26 manya da yara a makarantar Firamaren Sandy Hook, daga baya kuma ya harbe kansa.
  • Agusta 2012: Wani dan bindigar ya harbe mutane shida a wani wajen bautar mabiya addinin hadaka na Sikh a garin Wisconsin dake nan Amurka.
  • Yuli 2012: Haka kuma wani dan bindiga dadin ya kashe wasu mutane goma sha biyu a wani gidan majigi dake Colorado a lokacin nuna fim din ‘Batman’.
  • Janairu 2011: Dan bindiga ya harbe mutane shida har lahira tare da jikkata dan Majalisar Amurka Gabrielle Giffords a Arizona.
  • Nuwamba 2009: Wani Likitan mahaikatan rundunar sojin Amurka ya kashe mutane goma sha uku a birnin Fort Hood na Jihar Texas.
  • Afrilu 2007: Wani dalibin Jami’ar Fasaha ta jihar Virginia ya kashe mutane 32 kafin daga baya shima ya kashe kansa.
  • Oktoba 2006: Wani dan bindigar ya kashe wasu ‘yan mata biyar a wata makarantar mabiya gargajiya tsantsa ta Amish a Jihar Pennsylvania, inda shima daga karshe ya hallaka kansa.
  • Janairu 2006: Wata tsohuwar ma’aikaciyar gidan kai wasiku a California ta kashe mutane takwas a wani harin banbarakwai, kasancewar ba’a saba ganin sun kai hari ba, daga baya kuma ta kashe kanta.
  • Afrilu 1999: WAsu daliban Babbar Sakandaren Columbine guda biyu sun kashe dalibai 12 da mai koyarwa daya, suka kuma kashe kansu bayan aika-aikar da suka yi.
  • Nuwamba 1991: Wani dan bindiga ya kashe membobin wata tsangaya a Jami’ar Iowa tare da wani dalibi kafin shima ya kashe kansa.
  • Oktoba 1991: Wani dan bindiga yak aura mota cikin wata mashakata a Texas tare da bude wutar da ya kashe mutane 23 tare da kashe kansa.
  • Agusta 1986: Wani dan bindigar ya kashe wasu ma’aikatan kai wasiku har guda goma sha biyu a Oklahoma tare da kashe kansa.
  • Yuli 1984: Wani dan bindiga dadin ya kashe mutane 21 a gidan cijn abinci na McDonald’s dake California, kafin daga baya ‘yan sanda suka bindige shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG