Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Da Amurka Ta Kai Ya Kashe Sojojin Gwamnati 15


Jami'an Ma'iakatar Tsaron Afghanistan sun tabbatar cewa wani harin da Amurka ta kai kan 'yan ta'adda a lardin Helmand ya yi kuskuren hallaka Sojojin Gwamnati akalla 15.

Wannan kuskuren ya faru a gundumar Gereshk, inda ake wani kazamin fada tsakanin 'yan tsageran Taliban da sojojin gwamnati, inda Amurka ta kashe sojojin gwamnatin Afghanistan 15.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaron Afghnistan Dawlat Waziri ya ce a yayin fadan, wani kamami mai lizami da jirgin Amurka mara matuki ya harbo ya fada kan wani wurin binciken ababen hawa na sojojin gwamnati da daren jiya Jumma'a. Ya gaya ma Muryar Amurka cewa wannan hari ya yi sanadin mutuwar sojoji akalla 15 da kuma raunata wani guda.

Kwamandojin sojin Amurka sun tabbatar cewa an kashe wasu jami'an tsaro 'yan Afghanistan da ke aiki tare da sojojin gwamnati Afghanistan. Jami'an sojin na Amurka sun fitar da takardar bayani mai bayyana al'amarin da "abin takaici" sannan su ka yi alkawarin gudanar da bincike don sanin musabbabin faruwan al'amarin.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG