Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buratai Ya Bada Wa'adin Kwanaki A Kawo Shekau A Mace Ko A Raye


Babban hafsan Sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ba kwamandan rundunar yaki da kungiyar boko haram Operation Lafiya Dole wa'adin kwanaki 40, ya kawo masa Shekau a mace ko a raye.

A ranar juma'a 21, ga watan yuli, shugaban rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya umurci shugaban rundunar dake yaki da boko haram Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, wa'adin kwanaki arba'in ya kawo masa shugaban kungiyar boko haram Abubakar shekau a mace ko a raye.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Burgediya Janar Sani Kukasheka Usman, ya bayyana cewa babban hafsan sojojin ya umurci rundunar da ta tabbatar ta zakulo Abubakar Shekau a duk inda yake cikin wadannan kwanaki 40 ko da rai ko ba rai.

Ya kuma bukaci al'umma da ta taimaka da duk wasu bayanai da zasu taimaka wajan gudanar da wannan aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG