Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Cire Hamas Daga Jerin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda


Wasu matasan Falasdinawa rike da tutar gwagwarmayar kungiyar Hamas
Wasu matasan Falasdinawa rike da tutar gwagwarmayar kungiyar Hamas

Wata kotun kasar Masar ta yi watsi da hukuncin da wata kotu ta yanke na ayyana kungiyar reshen Hamas a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Ya zuwa yanzu babu dai wani martani da gwamnatin kasar da kungiyar ta Hamas suka mayar game da wannan hukunci da kotun ta yanke a yau Asabar.

A watan Fabrairun da ya gabata, kotun ta Masar ta ayyana kungiyar ta Hamas a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, wata guda bayan da aka saka reshen mayakan kungiyar a matsayin hakan.

A ‘yan watannin nan, dangantakar gwamnatin Masar da Kungiyar ta Hamas ta samu cikas, tun bayan da dakarun kasar suka fara toshe hanyoyin karkashin kasa tsakanin yankin Gaza da arewacin Sinai.

Da yawa daga cikin ‘yan kasar ta Masar, na yiwa kungiyar ta Hamas kallon wani reshe ne na kungiyar Muslim Brotherhood da aka haramta, tun a lokacin Masar na mulkar yankin Gaza a tsakanin shekarun 1948 da kuma 1967.

A da, Masar na da kyakywar dangantaka tsakaninta da Hamaz a lokacin mulkin tsohon shugaba Muhammed Morsi da aka hambarar, wanda ya mulki kasar daga watan Yunin shekarar 2012 zuwa Yulin 2013.

Hukumar tattara bayanan sirri kasar Masar ta kasance ta na shiga tsakanin Isra’ila da Hamas, tun bayan da rikici ya barke a shekarar 2009 da 2012 da kuma 2014.

Da kuma tsakanin Hamaz da abokiyar hamayyarta Fatah a Falsadinu, wadda ke karkashin jagorancin Mahmoud Abbas.

XS
SM
MD
LG