Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane da Dama A Somalia


Otal din da aka kai harin kunar bakin wake a Mogadishu babban birnin Somalia
Otal din da aka kai harin kunar bakin wake a Mogadishu babban birnin Somalia

Jami'an Somaliya sun ce mutane da dama sun mutu ko kuma sun samu raunuka, bayan da mayakan al-Shabab su ka kai hari kan wani otal da ke Mogadishu ta amfani da wasu motoci biyu shake da bama-bamai da kuma harbe-harben bindigogi a jiya Laraba.

Dr. Abdulkadir Abdulrahman Aden, shugaban sashin motocin daukar majinyata a birnin Mogadishu, ya ce jami'an asibiti sun karbi gawarwakin mutane 28 ya zuwa yanzu.

Tun da farko, gwamnatin Somaliya ta ce wasu mutanen kuma fiye da 50 sun samu raunuka. Kungiyar 'Yan Jaridun Somaliya ta kasa ta ce cikin wadanda su ka samu raunuka har da 'yan jarida 7.

An fara harin ne tun daga karfe 9 na safe agogon yankin, lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bama-baman da ke makare cikin wata motar daukan kaya a harabar otal din na Dayah, a cewar wani ganau. Otal din na yawan ganin 'yan kasuwa da kuma 'yan Majalisar Tarayyar kasar.

Ministan Tsaron Somaliya Abdulrazak OMar Muhammad ya ce an boye bama-baman ne ta wajen lullube bayan motar daukan kayan da jibgin gawayi.

Nan da nan sai kuma wata motar ta sheko da wasu mayaka hudu dauke da bindigogi, wadanda su ka abka cikin otal din da sashinsa ya lalace, su ka yi ta musayar wuta da masu tsaron otal din. 'Yan bindigar sun kuma shiga wani ginin da ke daura da otal din su ka kashe wasu jami'an tsaro biyu.

XS
SM
MD
LG