Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Syria kan sansanin yan gudun hijira ya kashe mutane 30


Wurin da bam ya fada har ya kashe mutane 30

Sa'o'i kadan bayan jami'an Rasha da Syria sun tabbatar da tsagaita wuta a birnin Aleppo sai jiragen yaki na Syria ko Rasha suka soma ruwan bamabamai kimanin kilimita 30 daga birnin lamarin da ya kaiga hasarar rayuka 30

Bamabaman sun fada ne akan sansanin da aka tanadawa 'yan gudun hijira kusa da iyaka da kasar Turkiya.

Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu a sansanin Kamouna kusa da Samada a yankin Idlib dake arewacin Syria kuma mutane da dama sun jikata sanadiyar hare-haren ta jiragen sama kamar yadda kungiyar dake hamayya da shugaba Assad ta sanar.

Hotunan da kungiyar ta nuna an ga wuraren da bamabaman suka rugurguza. Mai magana da yawun shugaban Amurka Barack Obama, Josh Earnest yace mutanen da aka kaiwa hari sun riga sun tagayyara saboda rashin muhallansu ya kaisu sansanin 'yan gudun hijira sai gashi kuma ana jefa masu bamabamai. Yace babu hujjar yin hakan.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka tace tana bukatar cikakken bayani akan lamarin tare da cewa ma'aikatar ta ga rahoton da yace gwamnatin kasar ce ta kai hare-haren.

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG