Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 12 Suka Mutu A Hari Da Aka Kai Wani Gidan Shakatawa


Hukumomi a kudancin Jihar California ta nan Amurka, sun tabbatar da kisan mutane 12 da wani mutun yayi a lokacin da ya harbe su, a cikin wani gidan shakatawa a daren jiya Laraba.

Babban sufeton ‘yansandan karamar hukumar Ventura, Geoff Dean, ya gayawa manema labarai cewa, daya daga cikin ‘yansandan farko da ya isa wannan gidan shakatawar na Borderline Bar & Grill ne ya fara rasa ransa, bayanda ya shiga wurin.

A cewar hukumar, wannan dansandan mai suna Sgt. Ron Helus, wanda ya kwashe shekaru 29 yana aikin ‘yan sanda a karamar hukumar, ya mutu ne bayan da aka kai shi asibiti.

Akwai mutane da dama da suka jikkata, amma sufeton ‘yansandan yace ba za’a iya sanin yawansu ba, da yake da dama daga cikinsu su ne suka kai kansu asibiti.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG