Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Harkar Tsaro Bata Gwamnati ce Kadai Ba" - Inji Gwamna Shema


'Yan kato da gora.

Gwamnan wanda yake magana a hira da Muriyar Amurka yace matsalar tsaro al'amari ne d a ya buwayi duniya baki daya yau, ba Najeriya kadai ba.

Gwamna Ibrahim Sheme wanda ya bayyana haka a hira da Sashen Hausa na Muriyar Amurka a watannin baya, yace kusan ko ta ina aka duba, hatta a manyan kasashen duniya ana fuskantar matsalar tsaro.

Idan aka dawo gida Najeriya Gwamna Shema yace, akwai dalilai masu yawa da suke janyo tashe tashen hankula wadanda suka hada da rashin aikin yi, talauci, da kuma 'yan ta'adda msu tsallakowa daga kasashe makwabta su shuka barna cikin Najeriya su sake gudu su koma inda suke samun mafaka.

Domin a shawo kan wadannan fitintinu, Barrsiter Shehu Shema yace akwai buktar gwamnati ta karfafa matakan horaswa ga jami'an tsaron Najeriya da kuma sama musu kayan aiki.

Haka nan Gwamnan na Katsina yayi kira ga manyan kasashen duniya su tallafawa Najeriya a kokarinta na shawo kan wannan rikici.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:09 0:00

XS
SM
MD
LG