Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce ta Kwace Chibok Daga Hanun Boko Haram


Sojojin Najeriya (File Photo).
Sojojin Najeriya (File Photo).

A makon jiya ne mayakan sakan na kungiyar Boko Harama suka kama garin na Chibok inda su kwashi 'yan mata fiyeda metan a farkon shekaran nan.

Rundunar sojan Nigeria tace ta samu nasarar fatattakar yan yakin sa kan kungiyar Boko Haram daga garin Chibok, arewa maso gabashin Nigeria inda a farko wannan shekara aka sace fiye da yan mata dalibai dari biyu.

Jiya Asabar jami'an soja suka ce sojoji sun kwace garin daga hannun yan Boko Haram wadanda suka mamaye garin a ranar Alhamis.

A wannan shekara kungiyar Boko Haram ta mamaye wasu garuruwa a jihohin Borno da Adamawa da suna zata kafa daular Musulmi.

Rundunar sojan Nigeria da kungiyoyin taimakon jama'a sun samu nasarar kwato wasu yankuna ciki harda garin Mubi da aka kwace daga hannun yan Boko Haram a ranar Alhamis.

An ci gaba da fafatawa duk da tsagaita bude wuta da gwamnatin Nigeria ta bada sanarwar ta a ranar sha bakwai ga watan Oktoba. A wani hoton video daya gabatar Mallam Shekau yace ba'a kula wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba, kuma yan mata dalibai da kungiyar ta sace an Musultan dasu harma an aurar dasu.

XS
SM
MD
LG