Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harkokin Tsaro da Sufuri Na Tabarbarewa A Kudancin Kamaru


Hadarin jirgin kasa da ya auku nakon jiya a Kamaru inda mutane fiye da tamanin suka rasu tare da wasu da yawa da suka jikata
Hadarin jirgin kasa da ya auku nakon jiya a Kamaru inda mutane fiye da tamanin suka rasu tare da wasu da yawa da suka jikata

Biyo bayan rushewar gadar dake hanyar da ta hada Yaounde da Douala makon jiya da kuma mummunan hadarin jirgin kasa da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama yanzu kasar Kamaru na fuskantar matsaloli daga harkokin sufuri da tsaro

Yanzu dai gwamnatin Kamaru ta gina wata gada ta wucin gadi ta maye gurbin wadda ta rushe a kan hanya daya tilo da ta hada Yaounde fadar gwamnatin kasar da Douala garin da ya kasance birnin kasuwanci.

Ministan cikin gida Rene Sadi Emmanuel ya kai ziyarar ganin gadar wucin gadin da yadda aka ginata tare da ba mutane hakuri. Ya bukaci a yi hakuri a cewarsa komi zai gyaru.

Gada daya tilo da ta hada biranen Yaunde da Douala ta rushe
Gada daya tilo da ta hada biranen Yaunde da Douala ta rushe

Wani da Allah ya yiwa gyadar dogo shi da iyalansa da suka tsira daga hatsarin jirgin da ya auku ya yi jawabin gargadi. Yace tun kafin hadarin ya faru jikinsa ya soma fada masa cewa wani abu zai faru. Yace kodayake direban jirgin ya ga abun da faru saboda taragon karshe ne ya fara tsinkewa amma bai tsaya ba. Sun tsira amma basu san yadda suka fita ba saidai ikon Allah.

Yanzu gwamnatin Kamaru ta kafa wata kwamiti na musamman domin binciken hadarin jirgin da ya sa kasar tayi zaman makoki har na kwana ukku. Abun lura kuma shi ne yankin shi yake fama da rikicin 'yan adawa a kasar banda hare-haren Boko Haram.

Wani abun mamaki shi ne duk wani bala'i da ya auku a kasar shugaban kasar Paul Biya baya ziyartar wurin.

Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00

XS
SM
MD
LG