Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarin Kwale-Kwale Ya Halaka Mutum Sama da 10 Jihar Sakkwaton Najeriya


Hatsarin ruwa

Kasa da kwana goma da kifewar jirgin ruwa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 100 a jihar Kebbin Najeriya, an sake samun hatsarin wani kwale-kwale a jihar Sakkwato wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 13.

An samu hadarin kwale kwalen ne a garin Ginga na karamar hukumar Shagari a jihar Sakkwato wanda ya hallaka mutanen 13.

Tuni dai aka yi jana'izar mutanen kuma jama'a na ci gaba da yin ta'aziya ga iyalan.

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi, shi ma tsohon gwamnan Sakkwato kuma shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattawa , Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko na cikin daruruwan jama'ar da suka yi ta'aziya ga iyalan.

Bisa ga lura da yadda hatsarin kwale-kwale ke lakume rayukan jama'a, masana sun jima suna baiwa gwamnatoci shawarwari na yadda za'a iya shawo kan wannan matsalar.

Farfesa Bello Baudan ya bayar da shawara cewa hukuma ya kamata ta tanadi jiragen masu kyau da jama’a za su yi amfani da su don tsallake Kogi, saboda a kula da lafiyar mutane.

Kuma ya ce dole ne a tabbatar da cewa ba a masu lodi ya wuce ka’ida saboda nauyi da kifewa, da kuma tabbatar da lafiyar ruwan.

Wata kila idan aka mayar da hankali ga wadannan shawarwarin a samu saukin irin wadannan matsalolin.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00


Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG