Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kula Da Harkokin Fiton Kayaki Ta Raba Tallafi Ga Mabukata


Ofishin Shiyyar arewa maso yammacin Najeriya na hukumar kula da harkokin fiton kayayyaki ta kasa, wato Nigerian Shippers Council, ya samar da kayayyakin tallafi ga cibiyoyin kula da raunanan mutane da kuma Asibitin kananan yara a Kano.

Hukumar, wadda ke karkashin ma’aikatar harkokin sufuri ta tarayya na kula da lamuran fiton kayayyaki, wato hajar da ‘yan kasuwa kan sayo daga ketare zuwa cikin gida Najeriya, amma ta hanyoyin jiragen ruwa. Baya ga haka hukumar na kula da tsarin kafawa tare da kula da aikace-aikacen tashoshin nesa da teku a sassan Najeriya, da ake kira Dry Ports.

Gidan gajiyayyu na Shahuci a Kano da Asibitin kula da Mata Masu Lalurar Yoyon Fitsari a Kwalli, kana da Asibitin Kula da Lafiyar Yara na Asiya Bayero, su ne hukumar ta Shippers Council ta rarraba wa kayayyakin tallafin.

Wasu daga cikin tsofaffi da raunanan mutane a gidan gajiyayyu na Shahuci sun nuna farin cikinsu, inda hukumar ta Shippers Council ta kai injin janareta, da barguna da sabulan wanka, da tawul da fitilu da sauran kayayyaki.

Malam Munnir Dahiru Kurawa da ke zaman shugaban Gidan Gajiyayyun na Shahuci wanda aka kafa a shekarar 1962, ya ce gidan na jajiyayyu na taimaka wa mutane ne wadanda ba su da galihu.

Shugabar shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ta hukumar ta Shippers Council, Hajiya Karimatu Othman, ta ce zabar gidan gajiyayyu, Asibitin yara da na mata masu lalurar yoyon fitsari wata hikima ce ta tallafa wa rukunin mutane masu tsananin bukata.

Ga cikakken rahoton wakilin muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG