Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastam Ta Tallafawa 'Yan Gudun Hijira a Jihar Yobe


Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya
Hamid Ali Mai Ritaya Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya

Kwanturolan hukumar da ke kan iyakar Najeriya da Benin shiyar Seme, Muhammad Ali ne ya sanar cewa hukumar ta mika wadannan kayayyaki da suka hada da buhuhunan shinkafa da man girki, da sutura ga rundunar sojin Najeriya domin gabatarwa ga sansanonin 'yan gudun hijira a jihar Yobe.

Hukumar ta bayyana cewa ta bayar da wadannan kayayyakin ne bisa umarnin gwamnatin tarayya domin tallafawa 'yan gudun hijira a tashe-tashen hankulan da ake yi a sassa dabam-dabam na kasar, musamman a arewa maso gabas.

"Mun aikawa 'yan gudun hijira buhuhunan shinkafa dubu goma 12 wato tirela 20 kenan, da kuma man gyada jarka 1025, da buhuhunan sukari guda 500," in ji Ali

A wani bangaren kuma, hukumar mai kula da shiyar ta Seme, ta kama buhuhunan shinkafa da adadinsu ya kai na tirela 8 a makonni biyu da suka gabata.

Saurari cikakken rohoton Babangida Jibril

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG