Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastam Ta Bullo Da Sabbin Dokokin Aikin Fiton Kaya a Nijar


Taron Hukumar Kwastom a Nijar
Taron Hukumar Kwastom a Nijar

A jamhuriyar Nijar, hukumar kula da shige da ficin kaya ta kafa wasu sabbin dokokin aikin fiton kaya da nufin magance matsalolin da ake fuskanta a tsakanin jami’an kwastam da ‘yan kasuwa da kuma masu aikin sufuri.

Hukumar ta kwastam ta shirya wani taro domin bayyana wa wadannan bangarori muhimman sauye sauyen da aka zo da su.

Lura da yadda duniyar kasuwancin kasa da kasa ke kallon dokokin aikin kwastam da ake amfani da su a jamhuriyar Nijar a matsayin wani tsohon yayi.

Gwamnatin Nijar ta aiwatar da sauye sauye da nufin sassauta wahalhalun ‘yan kasuwa da masu motocin dakon kaya da jami’an kwastam da shine yasa kiran taron baje sabon kundin ga wadannan bangarori.

Kanar Mohamed Yacouba na daga cikin masu wannan aiki, ya ce an yi wannan doka ta Kwastam ne tun 1961 wanda yanzu yanayin kasuwanci ya sauya, kuma suma aikin kwastam ya sauya. Kuma muna cikin kungiyoyin ECOWAS da UEMOA da suka gyara dokokinsu wanda ya kamata muma mu gyara dokokinmu.

Yacouba ya kara da cewa da hukumar kwastan tana fito da dokokin ita kadai ta ce ayi amfani da su, amma wannan sabon kundi yanzu yasa duk wani abu da hukumar za ta yi sai sun kirawo ‘yan kasuwa kafin su aiwatar da su sabanin yadda yake a baya kawai ita kadai ta ke dokarta.

Yanzu kuwa kafin kayan su shigo cikin kasa za ka iya zuwa wajen hukumar kwastam ka gaya musu irin kayanka su baka izinin shiga da su.

Sakataren kungiyar masu shigo da kaya daga waje, Chaibou Tchombiano, ya ce ya gamsu da bayanan da ya ji a wajen taron kuma ba sa samun matsala yanzu da kwastam.

Tchombiano ya kara da cewa ya kamata a duba kasashen da suke makwabtaka da su a duba abin da suke yi muma mu koye su, kuma muna da labari tsakanin ‘yan kasuwa na irin abubuwan da suke yi mu bama yi, ya kamata a gyara don kasuwanci ya bunkasa.

Suma direbobin dakon kaya na daga cikin wadanda ke fama da matsaloli irin na kan hanya daga jami’an kwastom saboda haka suke fatan ganin sabon tsarin ya tanadi matakan magance masu matsalolin su.

Jigo a kungiyar direbobi, Ali Aboubacar, ya ce direbobi suna kawo musu kukansu cewa suna wata daya har zuwa wata hudu a wajen hukumar kwastam suna jira.

Kuma yanzu suna so su mika kokensu ga hukumar na a rika sauke kayan da direbobi suka dauko ana barinsu suna tafiya.

Tuni dai aka soma zartar da wadanan sabbin dokokin aikin kwastam saboda haka tawagar jami’ai ke shirin zagaya yankunan kasa domin fadakar da bangarorin da ke da hannu a sha’anin kasuwanci da na awon kaya.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG