Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kula Da Masu Tabun Hankali-WHO


FILE - Wani likita yana kula da marar lafiya a asibiti

Hukumar lafiya ta duniya tayi kira ga gwamnatoci su kare ‘yancin al’ummarsu dake da tabuwar hankali wadanda ake fuskantar wariya da kuma kuntatawa.

Hukumar lafiya ta duniya tayi kira ga gwamnatoci su kare ‘yancin al’ummarsu dake da tabuwar hankali dake fuskantar wariya da kuma kuntatawa.

Hukumar tayi wannan kiran ne yayinda ake kiyaye ranar tabuwar hankali ta duniya. Hukumar lafiyar tace miliyoyin mutane suna fama da ciwon tabuwar hankali a duniya. Bisa ga cewar hukumar, kimanin kashi goma sha uku cikin dari na marasa lafiya a duniya suna fama ne da tabuwar hankali.

Wani bincike da aka gudanar a kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Habasha sun nuna cewa, mutane dake fama da tabuwar hankali suna mutuwa da sauri da kimanin shekaru goma zuwa ishirin fiye da sauran al’umma. Jami’ar kula da masu tabuwar kwakwalwa a hukumar lafiya ta duniya Michelle Funk tace, sau da dama akan yi watsi da mutanen da ke fama da tabuwar hankali.

Tace basu samun kular da ya kamata, sau da dama kuma ana kuntata masu. Tace ana tauye hakinsu da kuma rashin mutunta su, muhimman ababan da zasu taimaka masu su sami sauki.

Tace, bincike a duk fadin duniya ya nuna cewa, masu tabuwar hankali da ake kwantarwa a asibitai suna fuskantar tashin hankali ta fanni dabam dabam da suka hada da cin zarafinsu da dauresu, da hanasu abinci da ruwan sha, da kyalesu cikin yanayin rashin tsabta, da dauresu a hanasu walwala, da kyaliya na tsawon shekaru, wadansu lokuta iya rayuwarsu. Tace ana samun wannan yanayin a dukan kasashen duniya.

Hukumar lafiya ta duniya tace masu tabuwar hankali da dama suna iya samun sauki, wadansu lokuta kuma su warke idan aka sami kwararru da zasu kula dasu yadda ya kamata su kuma biyan bukatunsu da suka hada da kyalesu su zabi abinda ransu ke so.

XS
SM
MD
LG