Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Mai Fataucin Kwayoyin Da Tramadol Na Naira Biliyan 9


Ugochukwu Nsofor Chukwukadibia
Ugochukwu Nsofor Chukwukadibia

Hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi a Najeriya ta kama kwayoyin Tramadol da kudinsu  ya kai na fiye da Naira biliyan takwas da miliyan dari takwas da sittin da daya.

Hukumar ta kai samamen ne a cikin gidajen wani mutum mai suna Ugochukwu Nsofor Chukwukabia dake rukunin gidajen Victoria Garden City a anguwan lekki dake Legas a lokacin wani samame da jami’an hukumar suka kai a ranar Juma'a.

Muggan Kwayoyin
Muggan Kwayoyin

Wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Baba Femi ya aikewa ‘yan jaridu tace an sami kwayoyin ne a wasu katan- katan na muggan kwayoyi sanfarin Tramadol da yawan sa ya kai fiye da miliyan 13 a birnin Legas.

Hukumar tace ta kama Mr Ugochukwu dake zama shugaban kanfanin motoci na autonation, wanda dama ta dade tana bibiyar sa, bisa zargin mu’amula da muggan kwayoyi a Najeriya.

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Mai Fataucin Muggan Kwayoyin
Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Mai Fataucin Muggan Kwayoyin

Wannan kame da hukumar ta NDLEA tayi yazo ne wata biyu bayan ta kama wani mai hadahadar muggan kwayoyin Chris Emeka Nzewi da abokin aikin sa a bisa zargin sarrafa kwayoyin methamphetamine duk dai a anguwan rukunin gidajen na Victoria Garden City.

Gidan Wani Mai Fataucin Muggan Kwayoyin
Gidan Wani Mai Fataucin Muggan Kwayoyin

Ko a makon da ya gabata sai da hukumar ta kone hodar iblis na biliyoyin naira data kama a birnin na Legas.

Tuni shugaban hukumar ya yaba da kokarin da jami'an hukumar ke yi na kama manyan masu safaran muggan kwayoyi a Najeriya, tare kuma da godewa hukumomin yaki da muggan kwayoyi na Amurka bisa taimakon da suke baiwa hukumar ta NDLEA a Najeriya.

XS
SM
MD
LG