Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NDLEA Ta Kame Wasu Mutane Biyar Masu Fataucin Miyagun Kwayoyi


Tambarin hukumar NDLEA
Tambarin hukumar NDLEA

Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta NDLEA tace ta kame wasu mutane dake kokarin safarar kwayoyi da tabar wiwi ga wasu ‘yan kungiyar Boko Haram dake a wasu kauyuka a jihar Borno.

Hukumar ta bayyana hakanne a lokacin da ta gurfanar da wasu mutane guda biyar da ake zarginsu da safarar kwayoyin. An dai kame mutane Uku a tashar motar Muna, inda sukayi kokarin daura kwayoyin mota domin safararsu. Su kuma sauran mutanen Biyu an kame su a karamar hukumar Biu dake kudancin jihar Borno.

Mr Ona Ogilegwu, wanda shike zaman kwamandar hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi, shine ya sanar da hakan ga manema labaru lokacin da ya gurfanar da mutanen, ya kuma ce suna ci gaba da saka ido don ganin suna samun nasara ga ire iren mutanen da suke da tabbacin cewa sune ke kaiwa ‘yan kungiyar Boko Haram kwayoyi.

Da yake yiwa wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda karin haske, daya daga jami’an hukumar Garba Mohammed Bala, yace anyi niyyar daukar kayan ne zuwa Gamboru, kuma an kama tabar wiwi har da wasu kwayoyi har kilo 288.

Kasancewar hukumomi na kokarin ganin an sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin sai gashi wasu mutane na kokarin daukar kwayoyi suna kaiwa ‘yan Boko Haram.

A cewar Barista Kaka Shehu Lawan, kwamishinan ma’aikatar Shari’a wanda kuma ya kasance shugaban kwamitin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da gwamnatin jihar Borno ta kafa, yace da zarar an gama yaki da Boko Haram, za a koma kan yaki da kwaya, kasancewar abin da ya hada da kan ‘yan mata zuwa matan aure dayawa daga cikinsu na amfani da kwaya.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

XS
SM
MD
LG