Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Kada Kuri'un Zaben Shugaban Kasa A Liberia


‘Yan kasar Liberia suna can suna zaben shugaban kasa, wanda ke zama zaben farko na gwamnatin demokuradiyya zuwa ga wata, bisa tafarkin mulkin demokaradiya a kasar cikin fiye da shekaru saba’in.

Fiye da mutane miliyan biyu da suka yi rajistar yin zabe a kasar Liberia, zasu zabi wanda zai gaji shugaba Ellen Johnson Sirleaf, shugabar kasa mace ta farko a Nahiya Afrika, wadda zata ajiye ragamar mulki bayan ta kammala wa’adin mulki karo na biyu kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.

Cikin 'yan takarar shugaban kasa ashirin da daya da suke son su gaji shugaba Sirleaf, harda mataimakin ta Joseph Bokai, da Geoge Weah, shahararren dan wasan kwalon kafa da shugaban masu hamaiya Charles Brumskine.

Mace daya take takarar shugabar kasa, yayinda wata mace kuma take takara a matsayin mataimakiyar shugaban kasar Jewwel Howard Taylor, tsohuwar matar tsohon shugaban kasa Charles Taylor, wanda aka yanke wa hukunci a sakamakon laifuffukan yaki da ke da alaka da rawar daya taka a rikicin kasar Saliyo makwafciyar Liberia.

Idan babu dan takarar daya samu kashi hamsin daga cikin dari na kuri’un da aka kada, za’a yi zaben fidda gwani a watan Nuwamba idan Allah ya kaimu

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG