Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar zaben Nigeria ta dakatar da gudanar da zaben Gwamnoni da ‘yan majalisa a jihohin Arewa biyu


Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya Prof. Attahiru Jega. (File photo)
Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya Prof. Attahiru Jega. (File photo)

Shugaban hukumar zaben Nigeria farfesa Attahiru Jega ya bada sanarwar jinkirta gudanar da zaben Gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da tun farko aka shirya za’a yi talata mai zuwa 26 ga watan Afrilu zuwa ran Alhamis 28 ga watan Afrilu mai zuwa.

A hirar da yayi da manema labarai yau Alhamis a birnin tarayya na Abuja, Farfesa Attahiru Jega, yace hukumar INEC, ta tsaida shawarar dage gudanar da zaben Gwamnoni a jihohin Kaduna da Bauchi domin kara lokacin tabbatar da karfafa matakan tsaron kare lafiyar masu kada kuri’a. Amma, tun da farko shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya jaddada cewar za’a gudanar da zabe a ran Talata mai zuwa, zaben da shine na karshe a zagayen zabukan da ake yi a Nigeria cikin shekarar 2011.A jawabin da ya yiwa al’ummar Nigeria ta kafofin sadarwa ran Alhamis, shugaba Goodluck Jonathan yace ya baiwa jami’an tsaron Nigeria umarnin karfafa daukan matakan tsaro domin maido da zaman lafiya, don haka shugaba Goodluck Jonathan yake karfafa cewa, bayan rikicin da ya biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasa da yanzu ya fara lafawa, ai babu wani dalilin da zai hana gudanar da zabe na gaba, wato zaben Gwamnonin jihohi da na ‘yan majalisar wakilai.Kungiyar agaji ta Red Cross ta bada rahoton cewar rikicin siyasar da ya biyo bayan sakamakon zaben shugaban Nigeria ya janyo jikkatar mutane masu yawa. Da yawakuma sun rasa muhallinsu.

XS
SM
MD
LG