Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi A Najeriya Sun Ce Bam Ya Tashi A Kaduna


Soja yana binciken wata mota a Kaduna, ranar Alhamis, 21 Afrilu, 2011.
Soja yana binciken wata mota a Kaduna, ranar Alhamis, 21 Afrilu, 2011.

Amma kuma majiyoyin tsaro sun ce mutane biyu dake harhada bam din ne suka mutu lokacin da ya tashi musu haka kwatsam

Hukumomi sun ce wani bam ya tashi a yankin arewacin Najeriya, inda a wannan makon mutane da dama suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shugaban kasa.

Majiyoyi na tsaro sun ce bam ya tashi cikin daren jiya jumma’a a Kaduna. Kamfanin dillancin labarai na Reuters yace mutane akalla biyu wadanda suke kokarin hada bam din, sune suka mutu a lokacin da wannan bam ya tashi haka kwatsam.

Tarzoma ta barke wannan makon a yankin na arewacin Najeriya a bayan da aka sanar da cewa shugaba Goodluck Jonathan shi ne ya lashe zaben ranar asabar. Kafofin labarai sun ce an kashe mutane fiye da 100 a tashin hankalin, koda yake hukumomi sun ki su bayyana adadin wadanda aka kashe bisa fargabar cewa hakan na iya haddasa sabuwar fitina.

Hukumomi sun jinkirta zaben gwamnoni a jihohin Bauchi da Kaduna har sai ranar alhamis domin a kara samun lokaci na kwantar da hankulan jama’a.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Human Rights Watch" ta yi kira ga shugabannin Najeriya da su tabbatar da cewa jami’an tsaro ba su wuce gona da iri ba wajen kwantar da tarzomar ta bayan zabe. An ce shugaba Jonathan zai tura karin dakarun tsaro zuwa yankin. Amma wani mai bincike na kungiyar Human Rights Watch, Eric Guttschuss, ya fadawa VOA cewa dakarun tsaro na Najeriya sun saba wuce gona da iri a duk lokacin da aka tura su domin kwantar da wutar wata fitina.

XS
SM
MD
LG