Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi a jihar Arizona sun ce 'yar majalisar wakilai aka tsinkaya a harin da aka


Hoton 'yar majalisar wakilan Amurka Ganrielle Giffords (D-AZ) kewaye da kyandir a harabar asibitin Tucson University , Arizona, 08 Jan 2011.

Hukumomi a jihar Arizona sun ce 'yar majalisar wakilai aka tsinkaya a harin da aka kai lokacin da take ganawa da 'yan mazabarta.

Hukumomi dake bincike harbe harben jiya asabar da ya yi sanadin asarar rayuka a jihar Arizona dake kudu maso yammacin Amurka sun hakikanta cewa ‘yar majalisar dokokin tarayyar kasar ce aka tsinkaya da harin. Babban jami’in rundunar yansandan karamar hukumar dake gudanar da binciken, Clarence Dupnik ya shaidawa manema labarai jiya asabar cewa, dan bindigan ya yi niyar kashe ‘yar majalisar Gabreille Gifforda ‘yar jam’iyar Democrat ne lokacin da ya bude wuta a kofar wani shagon sayen kayan abinci dake yankinta, ya kashe mutane shida da suka hada da wani alkalin tarraya da kuma wata karamar yarinya ‘yar shekaru tara. Giffords ‘yar shekaru arba'in tana ganawa ne da mutanen mazabarta a shagon lokacin da aka bude wutar da ta rutsa da mutane goma sha tara. Har ya zuwa safiyar nan Giffords tana dakin gobe da nisa sakamakon harbinta da aka yi a ka. Jami’ai suna kyautata zaton zata warware. An bayyana wanda ya bude wutan a matsayin Jared Loughner, wani dan shekaru ashirin da biyu. A halin da ake ciki kuma jami’an gwamnatin Amurka suna ci gaba da bayyana takaicin harbin. Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana harin a matsayin wani bala’i ga kasar baki daya. Kakakin majalisa John Boehner ya ce harin ya razana shi, ya kuma bayyana shi a matsayin rashin hankali. Shugabar marasa rinjaye Nancy Pelosi ita ma tayi Allah wadai da harin da ta bayyana a matsayin bala’i ga kasa. A nata bangaren, sakatariyar tsaron Amurka Janet Napolitano, tace irin wannan rashin hankalin bashi da wurin zama tsakanin al’umma. Tsohon dan takarar shugaban kasa Sen John McCain mai wakiltar jihar Arizona, ya bayyana harbin Gifford a matsayin wani mummunan bala’i da ya firgita shi da kuma kasa. Gwamnan jihar Arizona Jan Brewer yace jihar tana bakin ciki ainun da wannan hatsarin, ya kuma bayyana Giffords a matsayin wakiliyar al’umma mai halin jinkai.

XS
SM
MD
LG