Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Tsaron Amurka ya Share Fagen Tattaunawa a China


Sakataren Tsaron Amurka Robert Gates, daga dama, lokacin da ake bikin isarsa China. Daga hagu kuma shi ne Ministan Tsaron China Liang Guanglie

Ministan Tsaron China ya fadi yau Litini cewa ya yadda da Sakataren Tsaron Amurka Robert Gates cewa akwai bukatar su inganta dangantakar sojojin kasashen nasu.

Ministan Tsaron China ya fadi yau Litini cewa ya yadda da Sakataren Tsaron Amurka Robert Gates cewa akwai bukatar su inganta dangantakar sojojin kasashen nasu.

To sai dai bai bayar da tabbacin cewa ba za a sami tangarda ba. Wannan al’amari na da muhimmanci ga Gates wanda ya jima yana nuna damuwa game da yanke huldar soji da China ta yi don ta bayyana bacin ranta game da sai da kayan yaki da Amurka ta yi wa Taiwan.

Gates, wanda ya je Beijing don farfado da huldar soji bayan ta yanke na tsawon shekara guda, ya gaya wa manema labarai yau Litini cewa das hi da Ministan Tsaron China Liang Guanglie ra’ayinsu ya zo daya game da bukatar dangantakar soji ta kud da kud don a kaucewa yiwuwar rashin fahimta ko kuma kuskure. Ya ce yakamata wannan cudanyar ta zama wadda canjin al’amuran siyasa ba za su shafe ta ba.

Liang ya fadi a wannan taron manema labaran cewa shima ya gwammce yarjajjeniyar tsaro mai dorwa. To amman bai kawar da zaton yiwuwar tabarbarewar dangata muddun aka sake sayar ma Taiwan kayan yaki ba, ya ce sayar da irin wannan kayan fadan na barazana ga muhimman muradan China.

China ta gayyaci Gates bara, to amman sai ta soke gayyatar ta kuma yanke huldar sojojin kasashen biyu bayan da Amurka ta shiga yarjajjeniyar sayar ma Taiwan kayan fada na dala biliyan 6 a watan Janairu.

XS
SM
MD
LG