Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 71 Sun Halaka A Hatsarin Jirgi A Iran


Masu aikin ceto da suka isa inda jirgin fasinjar kasar Farisa yayi hatsari.

Jirgin saman Fasinjan kasar Parisa/Iran yayi hatsari a dalilin rashin kyawun yanayi a yankin Arewa maso yammacin kasar jiya lahadi.

Jirgin saman Fasinjan kasar Parisa/Iran yayi hatsari a dalilin rashin kyawun yanayi a yankin Arewa maso yammacin kasar jiya lahadi, fasinja akalla saba’in da daya ne suka halaka daga cikin fasinja dari da shida dake cikin jirgin saman.

Anji shugaban kungiyar agaji ta kasar Iran, Mahmud Mozaffar yana bayani ta kafar labarun Telbijin na kasa cewa an sami Karin mutane Talatin da biyar da suka jikkata a dalilin hatsarin jirgin saman lokacin da jirgin yayi kokarin saukar gaggawa a kusa da birnin Urumiyeh, mai tazarar kilomita dari bakwai Arewa maso Yammacin birnin Tehran.

XS
SM
MD
LG