Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi a Najeriya sun tura sojoji a wani kauyen jihar Plateau sakamakon kashe mutane 13 a wani hari da aka kai daren jiya


Wadansu da suka jikkata a harin da aka kai a Jos, Nigeria. (File photo)

Hukumomi a Najeriya sun tura sojoji a wani kauyen jihar Plateau sakamakon kashe mutane 13 a wani hari da aka kai daren jiya.

Hukumomi a Najeriya sun tura sojoji a wani kauyen jihar Plateau sakamakon kashe mutane goma sha uku a wani hari da aka kai daren jiya. Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau tace an tura jami’an ne yau Talata zuwa kauyen Kuru-Wareng inda suka tabbatar da rahoton, yayinda kimanin mutane uku kuma suka ji raunuka. An yi fama da tashe tashen hankali a yankin Jos tsakanin Musulmi da Kirista. Jos shine babban birnin jihar Plateu wanda yake tsakanin arewacin kasar da musulmi suka fi rinjaye da kudanci inda kirista suka fi rinjaye. A kalla mutane tamanin suka mutu a jajibirin Kirsimati sakamakon harin bom da kungiyar Islama mai tsattsauran ra’ayi, Boko Haram ta kai .

XS
SM
MD
LG