Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar PDP Mai Mulki A Najeriya Ta Tantance Mutum Uku A Zaben Fidda Dan Takararn Shugaban Kasa


Shugaban kasa Jonathan, daga hagu,da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar

Shugaban kasa Goodluck Jonathan, zai kara da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar,da kuma tsohuwar hanu a siyasar kasar Sarah Jibril.

Jam’iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta tantance ‘yan takara uku a zaben fidda dan takara daya da zai wakilci jam’iyyar a zaben kasa da a’a yi cikin watan Afrilu.

Shugaban kasa Goodluck Jonathan zai kara da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar,da kuma tsohuwar hanu a siyasa Sarah Jibril. Wasu ‘yan jam’iyyar PDP uku sun kalubalanci takarar mr. Jonathan, amma wata kotu a Abuja ta yi watsi da karar ranar litinin.

Ahalin yanzu kuma,an kashe akalla mutane 18 a tsakiyar kasar a barkewar sabuwar tarzoma bisa sabanin akida da ta halaka dubban rayuka cikin shekaru 10 da suka wuce. Hukumomi a jihar Plato sunce wasu mutane da adduna sun kashe mutane 13 cikinsu hard a mata da yara, jiya talata.

An kai harin ne goshin asubahi a kauyen Kuru Wareng,wanda galibin mazauna ciki kiristoci ne. An kashe wasu mutane biyar a wani hari na daban a Barikin ladi duka jiya Talata.

XS
SM
MD
LG